Isa ga babban shafi
Burundi

Nkurunziza ya samu kyakkyawar tarba a Bujumbura

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya dawo fadarsa ta shugaban kasa a Bujumbura bayan Sojojin da ke ma sa biyayya sun murkushe yunkurin juyin mulki a lokacin da ya je taron sasanta rikicin kasar a Tanzania. Shugaban ya samu tarba daga dimbin magoya bayansa a a kauyensa Ngoza wanda ke kusa da Bujumbura fadar gwamnatin kasar.

Shugaban Burundi da Sojoji suka yi yunkurin hambararwa ya samu tarba daga Magoya bayan shi a Bujumbura
Shugaban Burundi da Sojoji suka yi yunkurin hambararwa ya samu tarba daga Magoya bayan shi a Bujumbura REUTERS
Talla

 Nkurunziza ya yi jinjina ga dakarun kasar da suka murkushe yunkurin juyin mulki, tare da yin barazanar kawo karshen zanga-zangar adawa da matakinsa na neman wa’adi na uku.

A ranar Laraba ne Tsohon hafsan Sojin kasar Godefroid Niyombare ya jagoranci juyin mulki, a yayin da ‘yan adawa suka shafe makwanni suna gudanar da zanga-zanga domin adawa da matakin Shugaba Nkurunziza na zarcewa da mulki wa’adi na uku.

Sojojin da ke masa biyayya sun fatattaki Sojojin da suka nemi hambarar da gwamnatinsa, bayan sun sanar da juyin mulki a wata kafar yada labarai mai zaman kanta a Bujumbura.

An dai shafe sa’o’i 48 al’ummar kasar na cikin tsaka mai wuya, game da bangaren da ke rike da madafan ikon kasar.

Jagoran Juyin mulkin Niyombare ya shadawa Kamfanin dillacin labaran Faransa cewa zai mika kansa bayan an cafke manyan hafsoshin sojin da suka jagoranci juyin mulkin.

Zuwa yanzu dai ba a sana dadin mutanen da suka mutu bat un lokacin da aka kaddamar da juyin mulki a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.