Isa ga babban shafi
Burundi

Ana gwabza fada a Burundi

Rikici ya barke a Burundi tsakanin dakarun gwamnati da dakarun da ke biyayya ga tsohon babban hafsan sojin kasar wanda ya jagoranci juyin mulki domin hambarar da shugaba Pierre Nkurunziza da ‘yan kasar ke adawa da matakinsa na neman wa’adi na uku.

Harabar ginin kafar Radiyo a Bujumbura Babban birnin kasar Burundi
Harabar ginin kafar Radiyo a Bujumbura Babban birnin kasar Burundi RFI/Sonia Rolley
Talla

Wasu majiyoyin tsaro sun ce dakarun da ke biyayya ga shugaba Nkurunziza na gwabza fada a harabar kafar Telebijin din kasar a Bujumbura tsakaninsu da sojojin da suka kaddamar juyin mulki.

Majiyoyin sun ce Sojojin Gwamnatin sun kaddamar da farmaki dauke manyan makamai a ginin Babbar kafar Telebijin ta RTNB, kuma babban Hafsan sojin gwamnatin Kasar Rime Niyongabo da ke biyayya ga Nkurunziza ya karyata juyin mulkin a kafar radiyo.

A jiya Laraba ne dai Tsohon Hafsan Sojin kasar Janar Godefroid Niyombare ya sanar da kwace mulki, yayin da Pierre Nkurunziza ke halartar taron sasanta rikicin Burundi a Tanzania.

Yanzu haka kuma babu tabbaci akan bangaren da ke da iko da tafiyar da kasar.

Akalla masu zanga-zanga 20 suka mutu a arangamar da suka yi da jami’an tsaro a tsawon makwanni biyu da aka shafe ana zanga-zanga. Har yanzu kuma ana ci gaba da zanga-zangar a Bujumbura babbar birnin kasar.

Masu zanga-zangar sun ce matakin Nkurunziza na neman wa’adi na uku ya sabawa kundin tsarin mulki da yarjejeniyar Arusha da ta taimaka aka kawo karshen yakin basasa a kasar.

Majalisar Dinkin Duniya tace kimanin mutane 50,000 suka tsere daga Burundi don fargabar yiyuwar barkewar yakin basasa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.