Isa ga babban shafi
Burundi

EU da Amurka sun bukaci a dage zaben Burundi

Kungiyar Tarayyar Turai da Amurka sun bukaci a dage zaben kasar Burundi bayan mummunar zanga-zangar ta barke a kasar na nuna adawa da shirin shugaba Pierre Nkurunziza na yin tazarce.Kasashen sun yi kira ga gwamnatin Burundi su dauki matakan lalama domin sasanta rikicin kasar.

Zanga-zangar kin jini Nkurunziza a Burundi
Zanga-zangar kin jini Nkurunziza a Burundi REUTERS/Jean Pierre Aime Harerimana
Talla

Kiran a dage zaben da Amurka da Tarayyar Turai suka yi na zuwa ne a yayin da al’ummar kasar Burundi, suka bijerewa gwamnati na kawo karshen zanga-zangar adawa da matakin shugaban kasar, Pierre Nkurunziza na neman wa’adin shugabanci na uku a karagar Mulki.

Kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci mahukuntan kasar Burundi su bi hanyoyin lalama domin kawo karshen rikicin siyasar kasar, don kaucewa barkewar yakin basasa.

Yanzu haka wasu mambobin kungiyar Turai da suka hada da Hollande da Switzerland da Belgium sun dakatar da bawa Burundi kudaden tallafi domin gudanar da zaben.

Tuni dai shugabar kungiyar Tarayyar Afrika Nkosazana Dlamini-Zuma ta bukaci a jinkirta zaben saboda halin da kasar Burundi ta shiga.

Nkurunziza dai na fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya na janye kudirinsa na neman wa’adi na uku bayan ya shafe shekaru kusan 10 yana shugabanci a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.