Isa ga babban shafi
Burundi

Nkurunziza ya jaddada aniyarsa ta yin tazarce a Burundi

Shugaban Kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya shaidawa al’ummar kasar cewar zai tsaya takarar shugabancin kasar a zaben da za a yi a watan gobe, a dai dai lokacin kasashen duniya ke gargadin ya kaucewa matakin. Tuni shugabannin kasashen da ke Gabacin Afirka suka kira taron gaggawa a makon gobe don tattaunawa kan matsalar wadda tuni ta haifar da ‘yan gudun hijira sama da 40,000 da suka bar kasar zuwa Rwanda.

Masu zanga-zangar adawa da kudirin tazarcen shugaban Burundi Nkurunziza
Masu zanga-zangar adawa da kudirin tazarcen shugaban Burundi Nkurunziza AFP PHOTO / PHIL MOORE
Talla

Majalisar Dinkin Duniya tace mutanen kasar Burundi sama da 21,000 suka tsere zuwa kasar Rwanda tsakanin Assabar zuwa Lahadi saboda fargabar rikicin siyasa a cikin kasar.

Tun a farkon watan Afrilu ne Jam’iyyar CNDD mai mulki ta ba shugaban kasa Pierre Nkurunziza damar neman wa’adi na uku a zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 26 ga watan Yuni.

Tun a 2005 ne shugaban ke jagorantar kasar, yayin da ‘yan adawa ke bayyana cewa matakin tazarcen ya sabawa kundin tsarin mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.