Isa ga babban shafi
Burundi

Ana ci gaba da zanga-zanga a Burundi

Mutanen kasar Burundi na ci gaba da zanga-zangar adawa da matakin zarcewa da mulki da Shugaban kasar ke yi, bayan da Kotun Kula da tsarin mulki ta wanke shi domin zarcewa da mulki wa’adi na uku.

Mutanen Burundi na zanga-zanga
Mutanen Burundi na zanga-zanga AFP PHOTO/PHIL MOORE
Talla

Duk da cewa mataimakin shugaban kotun tsarin mulkin, ya ki sanya hannu cikin shawarar da kotun ta yanke, kuma ya tsere ya bar kasar, wannan bai hana gabatar da matsayin kotun ba, da sauran alkalan kotun su shida suka tsaida.

Masu bore dai sun ce ba su yarda ba, kuma zanga-zangan nuna kyamar matakin, yanzu ne ma suka fara.

Gwamnatin tace idan har sun jingine bore to kuwa za a sako wadanda ake tsare da su saboda shiga boren da aka kwashe sama da mako daya ana yi.

Boren ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 13 kafin wayewar safiyar yau Laraba.

Alkali Sylvere Nimpagaritse ya shaidawa kamfanin Dillancin labaran Faransa cewa ba karamin wahala suka sha ba domin wai su amincewa shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya zarce da mulkin kasar.

Ya zuwa yanzu mutane da dama suka jikkata, yayin da bayanai ke cewa jami’an tsaro na tsare da mutane kusan 600.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.