Isa ga babban shafi
Burundi

Sojoji sun kwace mulki a Burundi

Tsohon Babban hafsan Sojan Burundi Janar Godefroid Niyombare ya sanar da hambarar da gwamnatin Pierre Nkurunziza, bayan shafe makwanni ana zanga-zangar adawa da matakinsa na yin tazarce.

An shafe makwanni ana zanga-zanga Bujumbura, kasar  Burundi
An shafe makwanni ana zanga-zanga Bujumbura, kasar Burundi REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Janar Niyombare ya sanar da hambarar da gwamnatin Nkurunziza a kafar yada labaran kasar.

Janar Niyombare ya taba rike mukamin babban hafsan Soji, kafin a tube shi a watan Fabrairu, kuma ya kwace mulki ne bayan Nkurunziza ya kama hanya zuwa taron kasashen gabacin Afrika a Tanzania game da rikicin kasar.

Niyombare ya bukaci al’ummar Burundi su kare rayuka da dukiyoyin Jama’a.

A yau Laraba ne Shugabannin kasashen gabacin Afrika za su gudanar da taro a Tanzania domin tattauna rikicin Burundi inda aka shafe makwanni ana zanga-zangar adawa da matakin shugaban kasar Pierre Nkurunziza na neman wa’adin shugabanci na uku.

Akalla masu zanga-zanga 20 suka mutu a arangamar da suka yi da jami’an tsaro a tsawon makwanni biyu da aka shafe ana zanga-zanga. Har yanzu kuma ana ci gaba da zanga-zangar a Bujumbura babbar birnin kasar.

Masu zanga-zangar sun ce matakin Nkurunziza na neman wa’adi na uku ya sabawa kundin tsarin mulki da yarjejeniyar Arusha da ta taimaka aka kawo karshen yakin basasa a kasar.

Majalisar Dinkin Duniya tace kimanin mutane 50,000 suka tsere daga Burundi don fargabar yiyuwar barkewar yakin basasa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.