Isa ga babban shafi
Burundi

An murkushe yunkurin juyin mulkin kasar Burundi

Sojoji masu biyayya ga shugaba Pierre Nkurinziza na kasar Burundi, sun kama da dama daga cikin jagororin sojin da suka yi yunkurin juyin mulki a kasar. 

Sojojin gwamnatin Burundi na sintiri a Bujumbura
Sojojin gwamnatin Burundi na sintiri a Bujumbura REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

BURUNDI COUP LEADER'S DEPUTY SAYS PUTSCH HAS FAILED,

Sojoji masu biyayya ga shugaba Pierre Nkurinziza na kasar Burundi, sun kama da dama daga cikin jagororin sojin da suka yi yunkurin juyin mulki a kasar.

Mai magana da yawun sojojin da suka yi yunkurin juyin mulki Venon Ndabaneze, ya ce an kama akalla mutanensu uku cikinsu da Cyrille Nadayirukiye wanda ya bayyana kansa a matsayin mataimakin shugaban juyin mulkin Godefroid Niyombare.

Kafin nan dai, Cyrille ya ce dakaru masu biyayya ga gwamnati sun murkushe su.
Amincewa da Janar Cyrille Ndayirukiye ya yi na rashin samun nasarar yunkurin, na zuwa ne jim kadan bayan fadar shugaban kasar ta bayyana cewa shugaba Pierre Nkurunziza, da baya kasar lokacin da aka bayyana juyin mulkin, ya koma gida.

Shugaban na halartar wani taro a makwabciyar kasar Tanzaniya ne, lokacin da Janar Godefroid Niyombare ya kaddamar da juyin mulkin, bayan da aka shafe makwanni ana zanga zanga a kan titunan kasar, don nuna adawa da yunkurin shi na zarcewa kan madafun iko karo na 3.

Yunkurin Juyin mulkin ya haifar da fargabar ci gaba da tashe tashen hankula a kasar, dake fama da talauci, a daidai lokacin da take kokarin farfadowa daga yakin basasan da aka shafe shekaru 13 ana gwabzawa.

Tuni Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da yunkurin juyin mulkin, yayin da Amurka ta ce Nkurunziza ta sani a matsayin shugaban kasar ta Burundi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.