Isa ga babban shafi
Burundi

AU na gudanar da taron gaggawa akan Burundi

Kungiyar tarayyar Afirka AU, na gudanar da taron gaggauwa a birnin Adis Ababa na kasar Habasha, domin tattauna halin da ake ciki a kasar ta Burundi.Taron na yau dai na zuwa ne, kwana daya da shugabannin kasashen yankin Gabashin Afirka suka gudanar da wani makamancinsa, jim kadan kafin sanar da cewa an kifar da shugaba Pierre Nkurinziza daga karagar mulki.

Janar Godefroid Niyombare ya yi sanar da Coup a Burundi
Janar Godefroid Niyombare ya yi sanar da Coup a Burundi REUTERS/Jean Pierre Aime Harerimana
Talla

Hakazalika suma Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya MDD, na gudanar da taron akan halin da Burundi ke ciki, adai-dai wannan lokaci da fada ke saka kansancewa a Bujumbura

Jakadan Majalisar a Burundi, ya ce yanzu haka ana kokarin tattaunawa shawo kan rikicin kasar cikin gaggawa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.