Isa ga babban shafi
Zambia

Shugaban Zambia ya fadi a bainar jama'a

Yau shugaban kasar Zambia Edgar Lungu ya yanke jiki ya fadi a kan mumbari, lokacin da yake jagorantar bukin ranar mata ta duniya, da aka yi a birnin Lusaka. Lamarin dai zuwa ne kasa da watanni 2 bayan Lungu ya karbi madafun ikon kasar, sakamakon mutuwar shugaban daya gabace shi Michael Sata.An garzaya da shugaban wani asbitin soja, sai dai fadar shugaban ta fidda wata sanarwar da ke cewa, yana fama ne da zazzabin cizon sauro, inda aka yi kira ga ‘yan kasar da kar su damu.Cikin ganawar da yayi da manema labaru, shugaban mai shekaru 58 a duniya yace sami sauki, kuma a cewar shi likitocin sun bayyana masa cewa yana fama da gajiya, inda suka bukaci ya huta.Shugaba Lungu yace likitocin sun yi masa karin gwaje gwaje, kuma yana fatan komawa gida don ci gaba da samun sauki.Cikin watan Junairu day a gabata Edgar Lungu ya karbi madafun ikon kasar, bayan mutuwar tsohon shugabamMichael Sata cikin watan Oktoban bara.Dama an yi ta yada jita jitar mutuwar Sata a wancan lokacin, lamarin da hukumomi suka yi ta musantawa, kafin daga bisa rai yayi halinsa.Sata shine shugaban Zambia na 2 da ya mutu a kan karagar mulki cikin hekaru 6, lamarin da ya sa ‘yan kasar ke kiran a rinka gajin ‘yan takarar shugabancin kasar, don tabbatar da lafiyarsu.Lungu, da ya fadi ne bayan ya tsaya kimanin mintoci 20, kuma ana jita jitar cewa yana fama da ciwon suga, sai dai mai magana da fadar shugaban Amos Chanda yace sakamakon gwajin da aka yi yana da kyau. 

Shugaban kasar Zambia, Edgar Lungu.
Shugaban kasar Zambia, Edgar Lungu. AFP PHOTO / CHIBALA ZULU
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.