Isa ga babban shafi
Sudan

Ana ci gaba da sulhu tsakanin gwamnati da ‘yan tawaye a Sudan

Bisa dukkanin alamu dai za’a sasanta, a ci gaba da tattaunawar da ake tsakanin gwamnatin kasar Sudan da kuma ‘yan tawayen Sudan Revolutionary Front da suka dade suna fada da gwamnati

RFI Hausa
Talla

Tsohon Shugaban kasar Afrika ta kudu Thabo Mbeki da ke shiga tsakani kan rikicin kasar Sudan, ya ce an samu ci gaba wajen tattaunawar da akayi a birnin Khartoum dan sulhunta rikicin kasar ta Sudan.

Bayan ganawa da ya yi da shugaba Oumar Hassan al Bashir, Mbeki ya ce sanya hannu kan yarjejeniyar da gwamnati ta yi da ‘Yan Tawayen na Sudan Revolutionary Front a makon jiya, wani ci gaba ne kan shirin tattauna kan makomar kasar.

Ita dai Jam’iyar adawa ta Umma party ta sanya hannu kan irin wanan yarjejeniya wadda za ta bada damar gudanar da taron kasa, inda za’a tattauna akan yadda za’a warware rikicin kasar.

A wani labarin kuma wata babbar ‘yar adawa a Siyasar kasar ta Sudan bangaren jam’iyyar Adawa, ta bayyana cewar ta
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.