Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire

An hana 'yan gudun hijirar Cote D'Ivoire shiga kasarsu

‘Yan asalin Cote D’Ivoire da yawansu ya kai 400 ne aka hana wa komawa gida bayan da suka yunkurin yin hakan daga makociyar kasar Liberia, wannan kuwa duk da cewa ‘yan gudun hijira na tare ne da rakiyar jami’an Majalisar Dinkin Duniya.

'yan gudun hijirar Cote D'Ivoire
'yan gudun hijirar Cote D'Ivoire
Talla

Tuni dai hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta koma wadannan mutane zuwa wani sansani da ke cikin Liberia yayin da ake ci gaba da tattaunawa da gwamnatin Ivory Caost kan wannan batu.

Kawo yanzu dai ana ci gaba da diga ayar tambaya a game da dalilan da suka sa Abidjan ta hana wa ‘yan kasar da ke zaune a Liberia tun 2011 komawa gida, duk da cewa hukumomi sun sha yin kira ga jam’a da su koma gida sakamkon kwanciyar hankali da aka sama.

Wata majiya a birnin Abidjan ta ce an hana shiga kasar ne domin ana fargabar cewa suna dauke da cutar nan ta Ebola da tuni ta kashe mutane da dama a Liberia, to sai dai hukumar kula da ‘yan gudun hijiar ta MDD ta ce wannan hujja ba ta gamsar ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.