Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire

An daure tsofaffin shugabannin cinikin Cocoa a Cote D'Ivoire

Wata Kotu a kasar Cote d’Ivoire, ta daure tsoffin shugabanin dake kula da cinikin coacoa a kasar, shekaru 20 a gidan yari, saboda samun su da laifin rub da ciki da kudaden kanfanin.Hukuncin kotun ya kawo karshen binciken da tsohon shugaban kasa, Laurent Gbagbo ya bada umurnin yi, saboda zargin almubazzaranci da kuma satar kudaden jama’a da ake zargin shugabanin hukumar da yi, wadda ta kunshi miliyoyin Dalar Amurka daga shekarar 2002 zuwa 2008.Kotun ta kuma wanke wasu mutane 13 da aka tuhume su tare, saboda an kasa tababtar da laifi akansu.Kasar Cote d’Ivoire itace kasa ta biyu da tafi arzikin Cocoa a duniya, inda take samar da kashi 35 na arzikin cocoan a kasuwannin duniya, kuma shine yake samarwa kasar kashi 40 na kudaden shigar da take samu.  

'Ya 'yan Cocoa
'Ya 'yan Cocoa Crédit : Nacivet
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.