Isa ga babban shafi
Sudan

An saki matar da ta yi ridda a Sudan

Mahukuntan kasar Sudan sun sake sakin Meriam Ibrahim da ta yi ridda bayan an cafke ta a tashar jirgin sama a Khartoum lokacin da ta ke shirin ficewa daga kasar. Yanzu haka ta samu mafaka a ofishin jekadancin Amurka a Sudan.

Meriam da ta yi ridda a Sudan da mijinta
Meriam da ta yi ridda a Sudan da mijinta Reuters
Talla

Mijin Matar Ba’amurke Daniel Wani da ya sa ta yin ridda ya shaidawa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa cewa sun samu mafaka tare da ‘Yan uwanta a ofishin jekadancin Amurka.

An tsare Meriam ne akan zargin ta yi takardun sheda na karya bayan kotu ta dage hukuncin kisa da aka yanke mata a ranar 15 ga watan Mayu.

Mijinta yace akwai sakwanni barazana ga rayuwar Matar da suke samu, akan haka suka nemi mafaka a ofishin jekadancin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.