Isa ga babban shafi
Sudan

Sudan: Amurka ta ce ba kama Meriam Yahia aka yi ba

Kasar Amurka ta musanta rahotannin dake cewa hukumomin Sudan sun sake kama Meriam Yahia Ibrahim, matar da aka sake bayan yanke mata hukuncin kisa, saboda samunta da laifin yin ridda. 

Meriam da mijinta
Meriam da mijinta Reuters
Talla

Wata babbar jami’ar gwamnatin Amurka da ake kira Marie Harf ce ta musanta rahotannin dake nuna cewa an sake kama Meriam Yahia Ibrahim, inda ta tabbatar da cewa an sanar da hukumomin Washington cewa ba a kama matar ba.

A cewar jami’ar, an dai tsare Meriam na dan wasu sa’oi a tashar sauka da tashi jirage dake Khartoum, inda aka yi mata tambayoyi kan takardunta na Viza.

A ranar litinin din da ta gabata aka sake Meriam bayan da aka yanke mata hukuncin kisa saboda yin ridda, lamarin da ja hankula kasashen duniya da dama.

A jiya Talata wasu rahotanni suka nuna cewa an sake kama Meriam ‘yar shekaru 26, yayin da take kokarin barin kasar ta Sudan tare da mijinta dan asalin kasar Amurka, sai dai Amurkan ta musanta wannan rahoto.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.