Isa ga babban shafi
Sudan

Hukuncin Bulala ya hau kan wata Mace a Sudan

Wata mace a sudan ta bayyana cewar a shirye take ta sha bulala a matsayin hukunci kin rufe gashin kanta, domin adawa da dokar kasar, inda take cewa ba za ta bi dokar da take ganin ta yan Taliban ne na rufe kanta ba.

Hoton Amira Osman Al-Hussein
Hoton Amira Osman Al-Hussein www.couriermail.com.au
Talla

Ga dukkan alamu dai Amira Osman Hamed zata fuskanci hukuncin bulala a ranar 19 ga wannna wata na satumba in har aka sameta da laifi, kamar yadda yake a dokar kasar Sudan, doka ce kowacce mace ta rufe gashin kanta, amma Amira yar shekaru 35 ta ki yin haka, lamarin da ya dauki hankalin masu rajin kare hakkin bil’adama a kasar.

An dai sameta ne da laifin a karkashin dokar kasar mai lamba 152 dake jaddada yaki da rashin shiga mai kyau a kasar.

A cewar Amira, wadda bazawara ce, mai kamfanin naura mai kwakwalwa ta Cumputer, so ake su zama kamar matan Taliba, kuma ba kowacce mace bace ke rufe kanta dan Allah ba, sai dan tsoron dukar da zai hau kanta.

A shekarar 2009 ne dai aka kama wata yar jaridar Lubna Ahmad al-Hussein da laifin sa wando wanda ya kai ga duniya ta bara akan lamarin, daga baya kuma kungiyar yan jaridar kasar suka biya tarar da aka sany amata, abinda ya sa aka sako ta, bayan ta kwana daya a kulle.

Haka kuma tarihi ya nuna an taba kama Amira da laifin shigar da kasar bata amince da shi ba a shekarar ta 2002 amma lauyarta ta biya tara aka sallameta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.