Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Sudan ta Kudu zata fuskanci Yunwa

Kungiyoyin agaji na duniya sun yi gargadin cewa al’ummar kasar Sudan ta kudu zasu shiga cikin wani mawuyacin hali na yunwa da cutuka kamar zazzabin cizon sauro da Amai da Gudawa saboda rikicin da ake yi a kasar da aka shafe tsawon watanni shida.

Likitocin MSF suna kula da lafiyar Mutanen Sudan ta kudu
Likitocin MSF suna kula da lafiyar Mutanen Sudan ta kudu REUTERS/Andreea Campeanu
Talla

Dubban mutane ne suka mutu a rikicin Sudan ta Kudu, yayin da Miliyoya suka kauracewa gidajensu saboda kazancewar rikici tsakanin dakarun gwamnati da Mayakan Riek Machar.

Kungiyar agaji ta Oxfam ta yi gargadin cewa al’ummar kasar zasu shiga mawuyacin hali na karancin abinci.

Tuni Majalisar Dinkin duniya ta yi irin wannan gargadin, tare da neman tallafin kudi domin taimakawa al’ummar Sudan ta kudu.

Majalisar Dinkin Duniya tace kimanin Yara kanana 50,000 na iya mutuwa a bana, idan har ba a dauki matakan kare aukuwar haka ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.