Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

MDD tana nazarin kafa kotun hukunta laifukan yaki a Sudan ta kudu

Sakataren Majalisar dinkin Duniya Ban Ki-moon yace akwai yiyuwar kafa wata kotu ta musamman, domin binciken wadanda ke da hannu a rikicin kasar Sudan ta Kudu, da ke fama da rikicin siyasa.

'Yan tawayen Sudan ta Kudu
'Yan tawayen Sudan ta Kudu Reuters
Talla

Wannan na zuwa ne yayin da bangarorin da ke yaki da juna ke zargin junansa da kaucewa shirin tsagaita wuta da aka yi.

Ban Ki-moon ya shaidawa kwamitin tsaro cewa akwai kyawawan hujoji da ke tabbatar da an aikata cin zarafin bil’adama a rikicin Sudan ta kudu, don haka ya zama dole a yi bincike tare da aiwatar da hukuncin da ya kamata.

Sai dai kuma yanzu dole ne a tsagaita wuta acewarsa domin bai wa ‘yan kasar damar komawa gidajensu tare da ci gaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali.

Tun a watan Disamban bara ne rikici ya barke a Sudan ta kudu bayan shugaba Salva Kiir ya zargi Riek Machar tsohon mataimakinsa da yunkurin kifar da gwamnatinsa. Kuma yanzu rikicin ya koma tsakanin kabilun shugabannin guda biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.