Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta ki tasiri

Gwamnatin Sudan ta Kudu da bangaren ‘yan tawaye, na zargin junansu kan karya yarjejeniyar da suka saka hannu ta tsagaita wuta, sa’oi kadan bayan da bangarorin biyu suka amince da dakatar da rikicin.

Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir tare da tsohon Mataimakinsa Riek Machar  kuma kwamandan 'Yan tawaye  a zaman sulhu a Addis Ababa
Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir tare da tsohon Mataimakinsa Riek Machar kuma kwamandan 'Yan tawaye a zaman sulhu a Addis Ababa EUTERS/Goran Tomasevic (
Talla

Bangaren ‘yan tawayen ne suka fara zargin dakarun kasar da kai musu hari a wasu garuruwa masu arzikin mai cikin har da garin Bentiu, inda suka zargi shugaba Salva Kiir da kaucewa yerjejeniyar da aka kulla.

Kakakin rundanar ‘yan tawaye Ruai Koang yace kaurcewa shirin yerjejeniyar tsagaita wuta, ba sabon abu ba ne a bangare gwamnati tare da zargin Dakarun Gwamnati da kai wasu sabbin hare hare akan ‘Yan tawaye.

Yayin da ‘Yan tawayen ke zargin gwamnati da tayar da rikicin, bangaren shugaba Kiir, sun ce ‘Yan tawaye ne suka fara kai harin domin an bai wa dakarun kasar umurni su tsagaita wuta.

Ministan yada labaran kasar Michael Makui yace a ranar Lahadi, ‘yan tawayen sun kai hare hare.

Wannan shi ne karo na biyu da shirin tsagaitwa wuta tsakanin bangarorin biyu ya ruguje domin a watan Janairu ma an cim ma irin wanna matsaya, amma ba ta yi tasiri ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.