Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Ana ci gaba da gwabza fada a Sudan ta kudu

Rahotanni daga Sudan ta kudu sun ce bangarorin da ke yaki da juna sun sake gwabza fada tsakaninsu, a yayin da kuma suke zargin juna da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da suka amince a birnin Addis Ababa na Habasha.

Dakarun Kungiyar SPLM ta gwamnatin Sudan ta kudu a garin Juba
Dakarun Kungiyar SPLM ta gwamnatin Sudan ta kudu a garin Juba Reuters/Andreea Campeanu
Talla

Rahotanni sun ce dakarun gwamnati da 'Yan tawaye sun sake gwabza fada a yankin Jahar Upper Nile mai arzikin fetir, a yayin da gwamnatin kasar ke zargin Mayakan Machar da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da suka amince a Addis Ababa.

Dukkanin bangarorin biyu da ke yaki da juna sun ruwaito cewa sun gwabza fada ne a yankin Malakal. kakakin 'yan tawaye ya zargi dakarun Gwamnati da fara takalarsu a lokacin da suke gudanar da fareti domin sauraren bahasi daga shugabanninsu akan batun yarjejeniyar da aka cim ma.

Dubban mutane ne suka mutu sakamakon rikici tsakanin shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Reik Machar. Mutane kuma sama da miliyan ne suka gujewa gidajensu.

Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa kasar Sudan ta kudu da ta balle daga Sudan zata fada cikin matsanancin hali na yunwa idan har ba'a kawo karshen rikicin kasar ba da yanzu aka kwashe tsawon watanni 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.