Isa ga babban shafi
Najeriya

Wai ina ne ake tsare da yan matan Chibok?

Neman inda ake tsare da wadannan da ‘yan mata 237, ko shakka babu shi ne babban abinda al’umma a cikin da wajen Najeriya ke fatar sani.Ko shakka babu inda lamarin ya faru, yanki ne da mai fadin gaske, ga sunkurmin daji sannan ga tsaunuka, yayin da a wasu lokuta sadarwa ke kansacewa abu mai wuya a tsakanin al’umma.  

Wasu daga cikin 'Iyayen Matan da aka sace 'yayansu a Chibok Jihar Borno a Najeriya.
Wasu daga cikin 'Iyayen Matan da aka sace 'yayansu a Chibok Jihar Borno a Najeriya. Reuters/Stringer
Talla

A dai-dai lokacin da wasu ke ganin cewa har yanzu wadannan ‘yan mata na ci gaba da kasancewa a wani wuri da ke Najeriya, wasu kuwa na ganin cewa tuni aka tsallaka da su zuwa kasar Kamaru mai makwabtaka da yankin mai fama da ayyukan kungiyar ta Boko Haram.
Za a iya cewa suna a Najeriya, domin kuwa garin Chibok ba ya da nisa da gandun dajin Sambisa ko a wani gandun mai suna Erwa, wadanda ke kumshe da manyan bishiyoyi da kuma tsaunuka, yayin da wasu ke cewa a lokacin da aka sace ‘yan matan, shiga kasar Kamaru domin fadawa gandun dajin Waza abu ne mai sauki, saboda bayanai na nuni da cewa ba wadataccin jami’an tsaron da za su iya hana faruwar hakan a lokacin.

To sai dai ko baya ga gano inda ake tsare da wadannan bayin Allah, wani babban aikin da ke gaba shi ne, yadda za a kwato su a cikin koshin lafiya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.