Najeriya
MDD zata gina sabbin Makarantu a arewacin Najeriya
Manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan bunkasa ilimi a duniya, tsohon Firaministan Birtaniya Gordon Brown, yace yanzu haka Majalisar na shirin gina makarantun boko har guda 500 domin bunkasa ilimi a yankin arewacin Najeriya mai fama da rikici. Brown, ya bayyana hakan ne a birnin Abuja inda ya ke halartar taron tattalin arzikin duniya da ake gudanarwa a karon farko a Najeriya, kamar yadda Muhammad Kabir Yusuf ya aiko da rahoto.
Wallafawa ranar:
Talla
Rahoto
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu