Isa ga babban shafi
Najeriya

Kasashen duniya za su taimaka don 'yanto 'yan matan Chibok

Kwana daya bayan da kasar Amurka ta bayyan cewa a shirye take da ta taimaka wa Tarayyar Najeriya domin ‘yanto ‘yan matan da kungiyar Boko Haram ta sace a jihar Borno, a yau laraba ita ma kasar Faransa ta ce a shirye take domin taimaka wa kasar shawo kan matsalar tsaro da take fama da ita.

Mata masu zanga-zangar neman a sako 'yan matan Chibok
Mata masu zanga-zangar neman a sako 'yan matan Chibok REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Farasa, ta bakin mai magana da yawun shugaban kasar stephane Le foll, ya ce kasar za ta yi abin da ya dace dan kubutar da da ‘yan matan da aka sace a garin Chibok, duk da cewa bai bayyana irin gudunmuwar da kasar za ta bayar a wannan yunkuri ba.

Le Foll, ya ce shugaba Francois Hollande ya bayyana sace ‘yan matan da cewa wani lamari ne mai matukar sosa rai da tada hankali,

A nata bangare kuwa, tun a jiya ne kasar Amurka ta sanar aikewa da wasu jami’an tsaron ta zuwa nigeria dan taimakawa kasar wajen ‘yanto wadannan ‘yan mata da aka ce yawansu ya haura 200,

Shugaba Barack Obama da kansa ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake zantawa da tashar talabiji ta CBS, inda yak ara da cewa abu na farko da Amurka ke fatan gani shi ne gaggauwa kwato wadannan ‘yan mata, sannan kuma dole ne a dauki matakai domin murkushe kungiyar ta Boko Haram.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.