Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta nemi Amurka ta dawo da kudaden Abacha

Gwamnatin Najeriya ta bukaci kasar Amurka ta dawo da kudaden Marigayi Janar Sani Abacha da suka kai dala Miliyan dari hudu da hamsin da takwas da ake zargin tsohon shugaban kasar ya sace zuwa asusu ajiyarsa a kasashen waje.

Tsohon Shugaban Najeriya Janar Sani Abacha
Tsohon Shugaban Najeriya Janar Sani Abacha AFP
Talla

A cikin wata sanarwa, Ministan Shari’a Mohammed Adoke, ya godewa Amurka na bankado kudaden da  Abacha ya ajiye a kasashen Turai da dama wadanda gwamnati zata yi amfani da su ga ci gaban mutanen Najeriya.

Ma’aikatar Shari’a tace tana tattaunawa da takwararta a Amurka domin mayar da kudaden zuwa Najeriya.

A ranar 5 ga watan Maris ne gwamnatin Amurka ta fitar da sanarwar kwace kudaden Marigayi Abacha amma ba tare da bayyana matakin da zata dauka ba akan kudaden.

Janar Sani Abacha ya kwashe kusan shekaru 5 yana mulki a Najeriya tsakanin 1993 zuwa 1998, wanda ya rasu saman mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.