Isa ga babban shafi
Nigeria

Ministar mai za ta gurfana gaban Majalisar wakilan Najeriya

Yau talata ministar man fetur a Nigeria, Diezani Alison-Madueke na gurfana a gaban majalisar wakilan kasar, don amsa tambayoyi kan zargin da ake yi mata na kashe kudaden gwamnati ba bisa ka’ida ba.

Diezani Allison-Madueke,ministar mai a Najeriya
Diezani Allison-Madueke,ministar mai a Najeriya AFP / Wole Emmanuel
Talla

Ana zargin ministar ne da amfani da kudin gwamnati wajen kula da jirgin sama na kashin kanta.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaba Goodluck Jonathan wanda ke ganawa da ‘yan Najeriya mazauna kasar Netherlands ke cewa ko shakka babu, kudin da yawansu yak ai dala bilyan 10 sun bata a kamfanin man fetur na kasar wato NNPC.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.