Isa ga babban shafi
Najeriya

Kungiyoyin Kwadago sun nemi Sanusi Lamido ya ajiye aikin shi

Kungiyoyin Kwadago a Najeriya sun bukaci a kori Gwamnan Bababn Bankin kasar, Sanusi Lamido Sanusi daga mukaminsa, bayan ya yi kira ga Gwamnatin Najeriya ta sallami rabin ma’aikatanta domin rage kashe kudade.

Abdulwaheed Omar, shugaban kungiyar kwadago a Najeriya lokacin da yake jawabin janye yajin aiki a kasar
Abdulwaheed Omar, shugaban kungiyar kwadago a Najeriya lokacin da yake jawabin janye yajin aiki a kasar REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Kungiyoyin kwadagon sun ce wannan ya nuna Sanusi baya da kwarewar iya aiki, da kuma rashin sanin assalin wadanda suke almubazzaranci da kudaden Gwamnati.

A lokacin da suke mayar da martani game da kalaman Sanusi kungiyoyin kwadago, NLC da TUC sun kare ma’aikata a matsayin wadanda ake zargi da lakume kudaden shigar da ake samu, suna masu zargin ‘Yan siyasa da sace kudaden gwamnati.

Dakta Mohammed Kabir Isa na Jmai’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ya shaidawa RFI cewa rage ma’aikatan ba tare da wani tanadi ba, zai haifar da babbar matsala.

A ranar Talata ne Gwamnan Babban Bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi, ya bukaci Gwamnatin kasar ta kori rabin ma’aikatanta, idan tana so ta bunkasa tattalin arzikin kasar, yana mai cewa duk kasar da ke kashe kashi 70 na kudaden shigarta wajen biyan albashin ma’aikata, tana cikin matsala.

A lokacin da ya ke jawabi a taron kwamitin bunkasa kasuwar Hannayen Jari a birnin Warri Jahar Delta, Mista Sanusi yace Gwamnatin Tarayya tana kashe kashi 70 cikin kudaden da take samu domin biyan albashin Ma’aikata.

Gwamnan Babban Bankin ya kuma koka kan yadda ake da Yan Majalisar Dattawa sama da 100, da wakilai 400, yana mai cewa kudaden da ake kashe wa ‘Yan Majalisa da bangaren zartaswa tare da ma’aikata, shi ke lakume kudaden da kasar ke samu.

Amma kuma kungiyoyi kwadago a Najeriya sun ce Sanusi bai cancanci mukamin shi ba, suna masu cewa Cin hanci da Rashawa da rashin shugabanci na gari su ne matsalolin da ke addabar tafiyar hawainiyar tattalin arzikin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.