Isa ga babban shafi
Najeriya

Sanusi Lamido ya nemi Gwamnatin Najeriya ta sallami rabin Ma’aikatanta

Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Sanusi Lamido Sanusi, ya bukaci Gwamnatin kasar ta kori rabin ma’aikatanta, idan tana so ta bunkasa tattalin arzikin kasar, yana mai cewa, duk kasar da ke kashe kashi 70 na kudaden shigarta wajen biyan albashin ma’aikata, tana cikin matsala.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi yana jawabi a Taron bunkasa tattalin arzikin duniya a Warwick
Gwamnan Babban Bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi yana jawabi a Taron bunkasa tattalin arzikin duniya a Warwick Wyap91/Open access
Talla

A lokacin da ya ke jawabi a taron kwamitin bunkasa kasuwar Hannayen Jari a birnin Warri Jahar Delta, Mista Sanusi yace Gwamnatin Tarayya tana kashe kashi 70 cikin kudaden da take samu domin biyan albashin Ma’aikata.

Gwamnan Babban Bankin ya kuma koka kan yadda ake da Yan Majalisar Dattawa sama da 100, da wakilai 400, yana mai cewa kudaden da ake kashe wa ‘Yan Majalisa da bangaren zartaswa tare da ma’aikata, shi ke lakume kudaden da kasar ke samu.

A bara Gwamnan babban Bankin ya gabatar da wata Kasida inda ya bayyana cewa kashi 25 cikin kasafin kudin Najeriya yana tafiya ne ga hidimar Majalisar Tarayya.

Sanusi Lamido yace akwai bukatar a diba yawan Kananan hukumomin da ake da su a Najeriya yana mai ra’ayin ganin an yi watsi da su don dogaro da Gwamnatin Jaha.

A cewar shi yawancin kudaden da Gwamnatin Jaha ke samu suna karewa ne wajen biyan Albashin Ma’aikata.

Sai dai kuma Gwamnan Jahar Delta Emmanuel Uduaghan ya soki kalaman Sanusi Lamido game da batun Korar Ma’aikata yana mai cewa idan har zasu dauki matakin sallamar Ma’aikata ya zama dole su samo wasu hanyoyin da Ma’aikatan za su taimakawa ci gaban Tattalin arzikin kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.