Isa ga babban shafi
Nigeria

Gwamnatin Najeriya ta sallami Sanusi Lamido

Gwamnatin Najeriya ta dakatar da Gwamman Babban Bankin kasar Sanusi Lamido Sanusi bisa laifin zarginsa da take dokokin aiki bayan ya zargi Kamfannin mai na NNPC da wawushe kudaden mutane dala biliyan 20 daga kudaden Tallafin Mai.

Gwamnan Babban bankin Najeriya Sanusi Lamido Aminu Sanusi
Gwamnan Babban bankin Najeriya Sanusi Lamido Aminu Sanusi
Talla

A watan Juni ne wa’adin Gwamnan babban Bankin zai kawo karshe, inda tuni aka nada mataimakiyar shi Sarah Alade domin maye gurbin shi.

Cikin wata sanarwar da ya fitar, mai taimakawa shugaban kasar, kan harkokin yada labaru da hulda da jama’a, Dr Reuben Abati, yace an dakatar da Sanusi ne saboda kashe kudaden gwamnati ba bisa ka’ida ba.

Tun lokacin da Sanusi lamido Sanusi ya fara fasa kwai, kan wasu kudaden da ake zargi sun bace daga kamfanin mai na kasar NNPC aka fara ganin yadda ya raba gari da hukumomi, musamman ma da shugaba Goodluck Jonathan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.