Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Amurka ta kwace kudaden Abacha

Kasar Amurka tace ta bayar da umurnin a rufe asusun ajiyar Tsohon shugaban kasar Najeriya Marigayi Janar Sani Abacha na kudi da suka kai dala Miliyan $458 da suka hada da na abokansa da suka boye a asusun kasashen waje.

Tsohon Shugaban Najeriya Janar Sani Abacha
Tsohon Shugaban Najeriya Janar Sani Abacha
Talla

Bangaren shari’a na Amurka yace akwai kudaden ajiyar Marigayi Abacha a kasashen Birtaniya da Faransa  kuma sun bukaci hadin kan kasashen domin rufe asusun ajiyar.

Janar Sani Abacha ya mutu ne a shekarar 1998, Kuma tun bayan mutuwarsa ake zargin ya wawushe kudaden al’umma.

Abacha ya zamo shugaban kasar Najeriya ne a ranar 17 ga watan Nuwamba a 1993 ta har juyin mulki kuma ya kwashe tsawon shekaru biyar yana shugabanci a Najeriya.

A cikin bayanan da Amurka ta fitar tace Mohammed Abacha da Abubakar Atiku Bagudu da sauran abokanan huldarsu sun kwashi Kudaden gwamnatin Najeriya zuwa Amurka domin sayen kadarori.

Amma babu wani bayani akan abin da zai biyo baya game da badakalar kudaden Marigayi Abacha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.