Isa ga babban shafi
Najeriya

Abdul Katako yace shaidar karya ya bayar a shari’ar Al Mustapha

Kwanaki bayan kamala shari’ar Manjo Hamza al Mustapha, da kuma yanke masa hukuncin kisa, daya daga cikin shaidun da aka yi amfani da jawabinsu, Mohammed Abdul Katako, yace shaidar karya ya bayar, saboda alkawuran kudade da gida da aka masa, amma yace yana neman gafara.

Manjo Hamza Al Mustapha tsohon dogarin Janar Sani Abacha da aka yankewa hukuncin Kisa.
Manjo Hamza Al Mustapha tsohon dogarin Janar Sani Abacha da aka yankewa hukuncin Kisa. Reuters
Talla

A cewar Katako ya bada shaidar Zur ne saboda alkawalin kudade kashi goma na kudaden da za’a karba hannun Muhammad Abacha.

Mista Katago ya shaidawa Rediyon Faransa cewa tsohon babban Jami’in tsaron SSS Kanal Kayode Are da Bola Ige da Yemi Oshibanjo ne suka tursasa masa bada shaidar karya.

A ranar 30 ga watan Janiru ne Wata babbar kotu a Jahar Legas a Najeriya ta yanke wa tsohon dogarin marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha hukucin kisa ta hanyar ratayewa sakamakon kama shi da laifin kisan Kudirat Abiola uwargidan marigayi MKO Abiola tsohon dan takarar shugaban kasa a zamanin mulkin Babangida.

Mai shari'a Mojisola Dada a babban kotun Legas tace an samu Manjo Hamza Al-Mustapha da hannu wajen shirya kisan Kudirat uwargidan dan siyasa marigayi Moshood Abiola.

A ranar 4 ga watan Yuni ne shekarar 1996 aka kashe Kudirat Abiola a birnin Lagas, a zamanin mulkin Sani Abacha. Mijinta Abiola shi ne ake hasashen ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a shekarar 1993 zamanin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida kafin soke sakamakon zaben.

Shari'ar Hamza Al mustapha ta ja hankalin al’ummar Najeriya matuka, musamman ganin lokacin da aka shafe ana gudanar da ita.

03:25

Bakonmu a Yau: DR Bawa Abdullahi Wase

Garba Aliyu

Akwai dai dimbin shaidu da aka samu da ke danganta su Al Mustapha ne suka kashe kudirat. Kuma Muhammad Abdul Katako yana daya daga cikin mutanen da suka bada shaida a gaban kotu.

Sai dai Mista Katako yace akwai gida da aka gina masa a Garin Jos saboda shaidar shi a gaban Kotu amma yanzu ya karyata kalaman da ya gabatar a kotu bayan yanke wa Al Mustapha hukuncin Kisa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.