Isa ga babban shafi
Najeriya

kotu ta yankewa Al Mustapha hukuncin Kisa a Najeriya

Wata babbar kotu a Jahar Legas a Najeriya ta yanke wa tsohon dogarin marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha hukucin kisa ta hanyar ratayewa sakamakon kama shi da laifin kisan Kudirat Abiola uwargidan marigayi MKO Abiola tsohon dan takarar shugaban kasa a zamanin mulkin Babangida.

Manjo Hamza Al Mustapha tsohon dogarin Janar Sani Abacha da aka yankewa hukuncin Kisa.
Manjo Hamza Al Mustapha tsohon dogarin Janar Sani Abacha da aka yankewa hukuncin Kisa. RFI/Hausa/Bashir
Talla

Hamza al Mustapha

Mai shari'a Mojisola Dada a babban kotun Legas tace an samu Manjo Hamza Al-Mustapha da hannu wajen shirya kisan Kudirat uwargidan dan siyasa marigayi Moshood Abiola.

Kotun kuma ta yanke hukuncin kisa ga Lateef Sofolahan na hannun damar Abiola ta hanyar ratayewa bayan kwashe shekaru ana shari’a tun a shekarar 1999.

A ranar 4 ga watan Yuni ne shekarar 1996 aka kashe Kudirat Abiola a birnin Lagas, a zamanin mulkin Sani Abacha. Mijinta Abiola shi ne ake hasashen ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a shekarar 1993 zamanin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida kafin soke sakamakon zaben.

Rehoton Salisu Hamisu

Salissou Hamissou

Shari'ar Hamza Al mustapha ta ja hankalin al’ummar Najeriya matuka, musamman ganin lokacin da aka shafe ana gudanar da ita.

Akwai dai dimbin shaidu da aka samu da ke danganta su Al Mustapha ne suka kashe kudirat.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.