Isa ga babban shafi
Najeriya

Harin Kano: Boko Haram sun aiko da sako amma Jonathan ya nemi sasantawa

Shugaban kungiyar Boko Haram Imam Abubakar shakau ya sake aiko da wani sako ta You Tube a Intanet inda ya yi ikirarin daukar alhakin kai harin Kano domin mayar da martanin muzgunawa mambobin kungiyarsu.

Shugaban Kungiyar Boko Haram a Najeriya Iman Abubakar Shekau a sakonsa ga shugaba Jonathan.
Shugaban Kungiyar Boko Haram a Najeriya Iman Abubakar Shekau a sakonsa ga shugaba Jonathan. REUTERS/IntelCenter/Handout
Talla

A Wani sauti da aka sako ta You Tube Imam Shekau yace “Mu muka kai hari, ni ne na bada umurnin kai harin kuma zamu ci gaba, “Allah Ya bamu nasara”.

Kakakin kungiyar, tun da farko ya bayyana daukar alhakin kai harin Kano da ya yi sandiyar mutuwar mutane 185 a ranar 20 ga watan Janairu.

Kodayake ba za’a iya tantance gaskiyar sakon ba, amma hoton ya nuna imam Shekau da muryarsa wanda ya aiko da sakon farko ga shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

A cewarsa, suna kai hare hare ne ga jami’an tsaro saboda Mambobinsu da matansu da aka cafke.

Imam Shekau ya yi wani gargadi ga Jami’an tsaron Najeriya cewa su sani suna da ‘Ya’ya da mata don haka zasu dauki fansa domin babu abun da ya fi karfinsu.

A cewarsa Sojoji a wata makarantar Islamiya a birnin Maiduguri, sun walakanta Al Kur’ani inda Shekau ya yi gargadi ga Sojojin cewa su sani suna da makarantun Sakandare da Firamare da jami’oi don haka suna iya mayar da martani.

Imam Shakau ya zargi Jami’an tsaro da kashe fararen hula tare da  zarginsu da aikata kisan. A cewarsa su basu yaki da fararen hula illa Jami’an tsaro da suka hada da Sojoji da ‘Yan Sanda.

Harin Kano ne dai mafi muni da ake zargin kungiyar Boko Haram da kai wa a birni mafi girma a arewacin Najeriya.

Imam Shekau shi ne wanda ake ganin mutum na biyu a rikicin kungiyar a shekarar 2009 kafin kashe shugabansu Muhammad Yusuf da Jami’an tsaro suka yi wa kisan gilla.

Rehoton Wakilin RFI Kabir Yusuf Daga Abuja

Kabir Yusuf

A wani Rehoto da Kungiyar kare hakkin Bil’adama ta Amnesty International ta fitar tace ‘Yan kungiyar Boko Haram sun kashe mutane kusan 1,000 cikin shekaru uku.

A jiya Alhamis ne shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana shirin sasantawa da kungiyar domin samun zaman lafiya.

Saboda magance matsalar tsaro a Najeriya ne Shugaba Jonathan ya maye gurbin Hafiz Ringim da MD Abubakar a matsayin sabon Sufeto Janar na 'Yan sanda saboda sakaci a zamanin Ringim inda dan kungiyar Boko Haram ya sulale hannun 'Yan Sanda bayan Cafke shi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.