Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram sun kashe mutane 935 a Najeriya, inji Amnesty

Kungiyar Amnesty International ta fitar da wani rehoton cewa, ya zuwa yanzu mutane kimanin 1,000 aka tabbatar da mutuwarsu a Najeriya, sakamakon hare haren da ake zargin kungiyar Boko Haram ke kai wa a cikin shekaru uku.

Shugaban Kungiyar Boko Haram a Najeriya Iman Abubakar Shekau a sakonsa ga shugaba Jonathan.
Shugaban Kungiyar Boko Haram a Najeriya Iman Abubakar Shekau a sakonsa ga shugaba Jonathan. REUTERS/IntelCenter/Handout
Talla

Kungiyar tace, a cikin wannan shekara ta 2012, mutane sama da 200 suka rasa rayukansu, abinda ke ci gaba da tada hankalin daukacin .Yan kasar, da sauran kasashen duniya.

A baya Gwamnatin Najeriya ta yi alkawarin tattaunawa da kungiyar domin kawo karshen harin, abinda ya sanya gwamnatin kafa wani kwamiti, wanda ya bata shawarwari, amma daga bisani matsayin ya sauya, inda Gwamnatin ke ikrarin magance matsalar wajen amfani da karfi.

Wannan matsayi ya saba da yadda wasu masana harkar tsaro ke bada shawara, inda suke cewa, ganin yadda ake ci gaba da rasa dimbin rayuka, ya dace a tattaunaa da wanan kungiyar.

Ko a ziyarar da ya kai don jajantawa mutanen birnin Kano, Shugabannin majalisar dokokin Najeriya sun nemi a yi wa 'ya'yan kungiyar Boko Haram ahuwa bisa hare-haren da suke kai wa a kasar a matsayin wata hanya ta yin rigakafin aukuwar haka nan gaba.

Shugaban Majalisar wakilai Aminu Tambuwal yace akwai bukatar a yi wa 'ya'yan kungiyar afuwa bisa abubuwan da suka aikata, domin samun zaman lafiya mai dorewa.

Shi ma a nasa bangaren shugaban majalisar dattawa Sanata David Mark, ya yi kiran yafewa wadanda suka kai hare-haren na Kano, a matsayin wata hanya ta magance matsalar zubar da jini da ya zama ruwan dare yanzu haka.

Sai dai kalaman nasu na zuwa ne bayan da shugaban kasar Goodluck Jonathan yace a shirye hukumomin tsaro suke su murkushe masu kai hare-haren na ta'addanci a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.