Isa ga babban shafi
Najeriya

Shugabannin kudanci sun nemi zaman lafiya a Arewacin Najeriya

Wasu gwamnonin jahohin Kudu guda biyar sun kai wata ziyara a garin Bauchi domin ganawa da takwarorinsu game da tashe tashen hankula da ake samu a wasu sassan Arewacin Najeriya, inda al’ummar kudanci a yankin ke fuskantar barazana da gargadin daukar fansa.

Gwamnan Jahar Imo Rochas Okorocha
Gwamnan Jahar Imo Rochas Okorocha RFI/saulawa
Talla

04:45

Rehoton Shehu Saulawa Daga Bauchi

Shehu Saulawa

Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha yana cikin gwamnonin da suka kai ziyarar kuma ya shaidawa Rediyon Faransa irin damuwar da al’ummar kudanci suke ciki a kudanci dangane da ‘Yan uwansu mazauna a yankunan arewaci.

Wannan ne karo na farko da gwamnonin kudancin suka kai ziyara a yankin Arewaci domin tattauna matsalar tsaro da ke addabar Najeriya.

Akwai yarjejeniya da shugabannin bangarorin biyu suka cim ma ta hanyar kai ziyara a yankunan biyu domin samun sasantawa da neman zaman lafiya a kasar.

Gwamnonin kudancin sun gana da al’ummarsu mazauna arewaci domin tattauna matsalolin da suke fuskanta tare da kwantar da hankalinsu.

A kwanan baya an samu wasu al’ummar arewaci da suka fara yin kaura daga yankin kudanci saboda barazana da suke fuskanta a yankin sai dai zaman taron na shugabannin ya danganta al’amarin a matsayin jita-jita ce babu wata barazana da ake samu a Jahohin kudancin kasar.

sai dai yanzu haka rehotanni daga Damaturu da ke Jihar Yobe, sun ce wasu ‘Yan bindiga sun kai hari kan wani jami’in tsaron farin kaya na SSS. Wani shaidar gani da ido Musa Adamu ya shaidawa Rediyo Faransa cewa bayan fitowarsu ne sallar Magariba suka ji karar bindiga tare din fashewa daga bisani ne kuma suka ji labarin kashe Jami’in tsaron.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.