Adamu Mu’azu ne sabon shugaban Jam'iyyar PDP a Najeriya
Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar PDP mai mulki a Najeriya ya tabbatar da Tsohon Gwamnan Jahar Bauchi Adamu Mu’azu a matsayin sabon shugaban Jam’iyyar kafin a gudanar da zabe bayan murabus din Alhaji Bamanga Tukur. Tuni dai aka rantsar da Mu’azu kuma Gwamnan Bauchi ne na yanzu Malam Isa yuguda ya mika sunan shi.
Wallafawa ranar:
A dokar Jam’iyyar PDP, kwamitin Zartarwa yana da ikon zaben shugaban riko don maye gurbin shugaban da ya yi murabus.
Mu’azu, Tsohon gwamnan Bauchi ne har sau biyu a 1999 da 2007, ya fuskanci suka a lokacin da Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya nada shi shugaban hukumar Fansho. Daga Abuja Aminu Manu ya aiko da Rahoto.
Rahoto: Adamu Mu’azu ne sabon shugaban Jam'iyyar PDP
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu