Isa ga babban shafi
Najeriya

Bamanga zai san makomarsa a Jam’iyyar PDP a Najeriya

Bayan da rahotanni a Najeriya suka ce shugaban Jam’iyyar PDP mai mulki Alhaji Bamanga Tukur ya mika takardar yin murabus, ana sa ran taron kwamaitin zartarwar Jam’iyyar ya yanke hukunci akan makomar shugaban wanda ke fuskantar matsin lamba.

Alhaji Bamanga Tukur,Shugaban Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya
Alhaji Bamanga Tukur,Shugaban Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Taron kwamitin amintattun Jam’iyyar da aka gudanar jiya laraba a fadar shugaban kasa bai yanke hukunci akan makomar shugaban Jam’iyyar na kasa ba.

Gwamnan Jahar Katsina Ibrahim Shehu Shema ya shaidawa RFI Hausa cewa taron Kwamitin amintattun bai tattauna batun Bamanga ba illa a saurari Majalisar Zartarwa.

Tun kafin fara taron na Amintattun Jam’iyyar PDP, Bamanga Tukur ya fito ya karyata labarin ya yi murabus amma daga baya wasu rahotanni suka ce shugaban Jam’iyyar ya mika takardar murabus din sa.

Alhaji Isa Tafida Mafindi, yana cikin kwamitin amintattaun jam’iyyar PDP kuma ya shaidawa RFI Hausa cewa Bamanga ya dauki shawarar yin murabus ba tare an tilasta masa ba domin daukar matakan dinkin barakar Jam’iyyar.

An dai shafe watanni Jam’iyyar PDP mai mulki na cikin rudani inda wasu gwamnonin Jam’iyyar suka canza sheka zuwa Jam’iyyar adawa ta APC kuma wasu suna zargin Bamanga a matsayin wanda ya haifar da matsalolin Jam’iyyar.

A yau Alhamis ne ake sa ran Majalisar Zartarwar Jam’iyyar zata yanke hukunci akan makomar shugabanta Bamanga Tukur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.