Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP a Najeriya ta Zabi Bamanga matsayin Shugaba

Jam’iyyar PDP mai mulki a Najeriya ta zabi Alh Bamanga Tukur matsayin sabon shugabanta bayan ‘Yan takara 10 sun janye masa wanda kuma shi ne dan takarar da ya samu goyon bayan Shugaba Jonathan Bayan kwashe makwanni ana tabka siyasa.

Alhaji Bamanga Tukur, Sabon shugaban Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya
Alhaji Bamanga Tukur, Sabon shugaban Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Kodayake Alh Bamanga Tukur bai samu goyon bayan wasu gwamnonin Jahohi ba da wasu manyan mambobin Jam’iyyar, amma shugaba Jonathan ya yi kokarin ganin Tukur ya cim ma nasara duk da sukar da ya ke fuskanta.

Rehotanni daga Abuja na cewa akwai ganawa ta Musamman da Jonathan da mataimakinsa Namadi Sambo suka gudanar tare da shugabannin Jam’iyyar domin neman masu takarar shugabancin Jam’iyyar da Bamanga sun janye.

Jam’iyyar PDP ta kwashe tsawon shekaru sama da goma tana mulki a Najeriya tun bayan da sojoji suka mika mulki ga farar hula a shekarar 2009 amma al’ummar Najeriya suna ganin babu wani abu na ci gaba da shugabancin jam’’iyyar ya samarwa Najeriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.