Isa ga babban shafi
Mali

Amurka, kungiyar tarayyar Turai sun yaba da zaben ‘yan majalisun Mali

Kasashen duniya da kungiyoyi na ci gaba da yabawa da zaben ‘yan majalisun kasar Mali da aka gudanar a karshen makon da ya gabata, inda aka yi kira ga hukumomin kasar, da su ci gaba da karfafa turbar dimokradiya.  

Lokacin da ake gudanar da zaben 'yan majalisu a kasar Mali a ranar Lahadin da ta gabata
Lokacin da ake gudanar da zaben 'yan majalisu a kasar Mali a ranar Lahadin da ta gabata REUTERS/Adama Diarra
Talla

Kasar Amurka ce dai ta fara jinjinawa zaben ‘yan majalisun, sannan itama kungiyar Tarayyar Turai ta bi sahu.

Itama kungiyar fararen hula ta Citizen’s Electoral Observation Deck a kasar ta Mali wadda ta tura masu saka ido kusan dubu hudu, ta ce wannan zabe abin a yaba ne.

Mafi aksarin masu tofa albarkacin bakinsu game da zaben sun fi yabawa ta ne da yadda aka gudanar da zaben ba tare da wani mummunan tashin hankali ba.

Inda a ada ake ikrarin ‘yan tawayen kasar za su kai hare hare a wasu sassan kasar.

Ko da yake rahotanni sun nuna cewa zanga zangar da ‘yan tawayen abzinawa suka gudanar a yankin Arewa maso gabashin garin kidal, ta hana mutane da dama kada kuri’unsu a yankin.

Zaben ‘yan majalisun shine zabe na baya bayan nan da aka gudanar a kasar ta Mali tun bayan zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Agusta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.