Isa ga babban shafi
Mali

An kai harin rokoki a Gao arewacin Mali

Rahotanni daga Mali sun ce da sanyin safiyar Alhamis an kai harin rokoki a garin Gao da ke arewacin kasar, lamarin da ke cusa shakku da fargabar matsalar tsaro a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaben ‘Yan Majalisu. Wata Majiyar tsaro a Gao tace da misalin karfe 5:00 na safe ne aka ji karar harbin na roka sai dai majiyar tace babu wani ta’adi da aka samu.

Wasu Tankokin yaki a yankin Gao arewain Mali
Wasu Tankokin yaki a yankin Gao arewain Mali REUTERS/Emmanuel Braun
Talla

Amma Majiyar Soji a Mali tace hare haren rokoki guda uku aka kai inda suka fada ruwa can wajen garin na Gao.

A ranar Lahadi ne kasar Mali ke shirin gudanar da zaben ‘Yan Majalisu bayan an kammala zaben shugaban kasa watanni uku da suka gabata.

Kasar Mali tana kokarin tayar da komada ne ta fannoni da dama bayan juyin mulkin Soji a 2012 wanda ya ba ‘Yan tawaye nasarar karbe ikon yankin arewacin kasar.

An kwashe watanni Tara, yankin arewaci yana hannun ‘Yan tawayen Abzinawa da mayakan Ansar Dine da MUJAO kafin dakarun Faransa su kwato yankin bayan kaddamar da yaki a watan Janairu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.