Ana zargin ‘Yan tawayen Abzinawa ne suka kashe Ma’aikatan RFI
Mai Gabatar da kara a kasar Faransa, Francois Molins, ya bayyana sunan Baye Ag Bakabo, daya daga cikin shugabanin Abzinawan Mali, a matsayin wanda ke da hannu wajen kashe ma’aikatan Rediyo Faransa biyu, Claude Verlon da Ghislaine Dupont. Jami’in yace an samu shaida a cikin motar da aka sace ‘Yan Jaridun da ke dauke da sunansa, kuma an ganshi yana tuka motar.
Wallafawa ranar:
Molins ya kara da cewar, wani kwamandan kungiyar Al Qaeda, Abdelkarim al Targui ne ya bayar da umurni sace ‘Yan Jaridun, a matsayin ramako kan yadda sojojin Faransa da Majalisar Dinkin Duniya suka kakkabe Yan Tawayen kasar a yankin arewaci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu