Jami’an tsaron Mali na ci gaba da tuhumar mutane tara game da kisan wakilan rfi
Jami’an tsaro a kasar Mali na cigaba da yiwa wasu mutane tara tambayoyi daga cikin wadanda ake zargin suna da hannu wajen kashe ‘Yan Jaridun Radio Faransa biyu, Claude Verlon da Ghislaine Dupont.
Wallafawa ranar:
Jami’an tsaron sun kuma gano mai motar da aka yi anfani da ita wajen sace ‘yan Jaridun kafin a hallaka su, inda aka bayyana sunansa a matsayin Ag Bakabo.
Ag Bakabo na daga cikin 'yan Tawayen Abzinawa dake neman kasa ta kansu wadda ake cewa tana da alaka da kungiyar Al Qaeda.
A makon da ya gabata ne aka kashe ‘yan jaridun biyu bayan sun kammala aiki a garin Kidal dake arwacin kasar ta Mali.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu