Isa ga babban shafi
Mozambique

Rundunar sojin Mozambique ta sanar da kwace wani sansanin ‘yan tawaye Renamo

Kasar Mozambique ta ce sojojin ta sun sake kwace wani sansanin kungiyar ‘Yan Tawayen Renamo, a wani hari da suke cigaba da kaiwa dan kakkabe su a cikin kasar.

Wasu 'yan tawayen kungiyar Renamo a Mozambique
Wasu 'yan tawayen kungiyar Renamo a Mozambique AFP PHOTO / JINTY JACKSON
Talla

Mai Magana da yawun fadar shugaban kasar, Edson Macuacua, ya ce an kai harin ne a Marinque dake tsakiyar kasar, abinda ya kai ga musayar wutar tsakanin bangarorin biyu.

Kasashen duniya na cigaba da bayyana fargabar barkewar wani sabon yakin basasa a cikin kasar.

A farkon makon nan dakarun kasar sun karbe sasanin ‘yan tawayen dake cikin dajin Sathundjira dake tsakiyar tsaunukan Gorongosa.

Wannan lamari ya yi sandiyar mutuwar wani na hanun daman shugaban Renamo, Afonso Dhlakma wanda ya tsira da kyar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.