Isa ga babban shafi
Mozambique

Za'ayi Rajistan Masu Wayan Hannu A Mozambique

Hukumomin kasar Mozambique na shirin yiwa dukkan wayoyin hannu dake kasar rajista da sunayen masu su, makonni kadan bayan wani kazamin bore a kasar, inda mutane 14 suka mutu sakamakon wani sako da akayi ta aikewa jama'a  ta wayan hannu.Ministan Sadarwa na kasar Paulo Zucula ya fadi yau cewa karkashin sabon dokan za'a karfafa sirrin sakonni ta yanar gizo da kawar da ayyukan hashsha.Farkon wannan watan aka tsinke kafar aikewa da sakonnin ta wayoyin hannu sakamakon kazamin boren daya biyo bayan wani sako da aka aikewa jama'a ta wayan hannun dake neman ayi bore saboda an kara farashin kudin burodi.Kusan mutane miliyan biyar ne daga cikin mutan kasar miliyan 20 keda wayoyin hannu. 

Tutar kasar Mozambique
Tutar kasar Mozambique rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.