Isa ga babban shafi
Mozambique

"Yan Sandan Mozanbique Na Tsare Da Mutane 286

‘Yan sandan kasar Mozambique na tsare da mutane 286 da suke zargi da hannu wajen mummunar zanga-zanga saboda hauhawan farashin kayan abinci, alamarin da ya kai ga mutuwar mutane 13 yayin da mutane samada 403 suka sami munanan raunuka.Zanga-zangan na kwanaki uku makon jiya ta kai ga fasa manyan shaguna 66 da Bankuna uku inda aka kwashi ganima a babban birnin kasar Maputo.Boren ya bazu zuwa sauran manyan garuruwan kasar, kamar yadda Rundunar ‘Yan sandan kasar ke cewa.Sanarwan ‘yan sandan na cewa ta wasiku a wayoyin hannu ne wadanda suka shirya boren suka gayyaci jama'a.Mai magana da yawun Rundunar ‘Yan sandan kasar Pedro Cossa bai ce ga takamaiman laifin da ake zargin wadanda ake tsare dasu ba.‘Yan Sanda biyar na daga cikin wadanda suka sami munanan raunuka.  

Masu bore a birnin Moputo na Mozambique
Masu bore a birnin Moputo na Mozambique rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.