Shugabannin Afrika ta Yamma sun nemi taimakon Dala miliyan 25 domin gudanar da zaben Mali
Shugabannin Kasashen Afrika ta yamma, sun bukaci kasashen duniya da su taimaka musu da tsabar kudi Dala miliyan 25 dan gudanar da zaben kasar Mali da aka shirya yi a karshen wannan wata.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan da takwaransa na Cote d’Ivoire, Alassane Ouattara ne suka bayyana haka, a taron da suki yi a Abuja.
Wannan kira na zuwa ne a dai dai lokacin da ake shirin kammala taron shugabanin kasashen Afrika ta Yamma a yau, inda suke nazari kan yadda za’a gudanar da karbabben zabe a kasar ta Mali, ba tare da samun tashin hankali ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu