Isa ga babban shafi
Mali

Tiebile Drame ya janye daga takarar neman shugabancin Mali

Daya daga cikin ‘yan takarar neman mukamin shugabancin kasar Mali wanda kuma ya taka gagarumar rawa domin samar da yarjejeniyar zaman lafiyar da azibinawan kasar, Tibile Drame, ya sanar da janyewarsa daga zaben da za a gudanar ranar 28 ga wannan wata na Yuli.

Tiébilé Dramé
Tiébilé Dramé AFP PHOTO / Ahmed Ouoba
Talla

Dan takarar, ya ce ya janye ne saboda ya fahinci cewa zai kasance abu mai wuya a gudanar da zaben a cikin kyakkyawan yanayi, inda ya yi zargin cewa ba za a iya kai kayan zabe a yankin Kidal kafin wannan rana ta 28 ga watan yuli ba.
Tun da jimawa ne dai aka soma hasashen cewa zai kasance abu mai wuya a iya gudanar da zaben na Mali a duk fadin kasar sakamakon rashin hukumomi a wasu yankuna na kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.