Isa ga babban shafi
Somalia

An cafke wani kwamandan mayakan Shabaab a Somalia

Mahukuntan kasar Somalia sun tabbatar da cafke Sheikh Hassan Dahir, daya daga cikin kwamandojin mayakan Al Shabaab, wanda yana cikin jerin sunayen ‘Yan ta’adda da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa takunkumi.

Cheikh Hassan Dahir Aweys, Shugaban Mayakan Hizbul Islam,a Somalia
Cheikh Hassan Dahir Aweys, Shugaban Mayakan Hizbul Islam,a Somalia (Photo : Reuters)
Talla

A wani yanki na tsakiyar Somalia ne aka cafke Sheikh Hassan Dahir Aweys wanda yanzu haka ke karkashin kulawar jami’an tsaro a wani gida da ke garin Adodo a kasar.

Sheikh Aweys yana cikin jerin sunayen ‘Yan ta’adda da Majalisar Dinkin duniya ta kakabawa takunkumi. Kuma yana cikin mutanen da Amurka ke nama ruwa a jallo.

Wasu dai suna ganin cafke Sheikh Aweys a dai dai wannan lokaci da kasar Somalia ke fuskantar hare hare, wani ci gaba ne ga gwamnatin Somalia.

Akwai dai yiyuwar gwamnatin Somalia zata iya zaman tattaunawa da Sheikh Aweys wanda aka ce yana jagorantar wani bangare na mayakan Al shabaab da suka balle.

Garin Adodo dai yana kusa da yankunan da ke karkashin ikon Sheikh Aweys, mahukuntan garin sun ce suna tattaunawa da Mogadishu domin yanke hukunci akan makomar shi

A baya  Uways shi ne babban kwamandan mayakan Somalia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.