Mali
Sojin Mali sun shiga garin Kidal yayin da aka fara yakin neman zabe a kasar
Yanzu haka sojojin kasar Mali sun yi nasarar shiga garin Kidal dake hannun ‘Yan tawaye, yayin da ake cigaba da shirin zaben shugaban kasa a karshen wannan wata.
Wallafawa ranar:
Talla
Rahotanni sun ce ‘Yan takara 24 sun fara yakin neman zabe, wanda za a gudanar a ranar 28 ga wannan wata na Yuli.
Wannan zabe shine na farko tun bayan hambarar da gwamnatin kasar a watan Maris din shekarar da ta gabata.
Wasu da dama dai na ganin an saka hanzari a gudanar da zaben kasar yayin da wasu ke ganin cewa lokacin ya yi da za a mayar da kasar kan turbara demokradiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu