Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Mugabe ya zargi ‘yan adawa da tsoron kayi a zabe

Shugaban Kasar Zimbabwe, Robert Mugabe, ya zargi abokan adawarsa da tsoron shan kaye da za su yi a zabe mai zuwa, a matsayin abin da ya sa suke neman jinkirta wanan zabe da aka shirya yi a karshen watan gobe.

Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe
Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe Reuters/Philimon Bulwayo
Talla

Mugabe ya shaidawa wata jaridar kasar cewar, babu abinda ya sa suke bukatar dage zaben sai tsoron shan kaye.

A dai karshen makon da ya gabata ne kasashen yankin a karkashin lemar SADC suka gudanar da wani taro a Mapotu na kasar Mozambique domin kaucewa barkewar rikicin siyasa a kasar ta Zimbabwe.

Su dai 'yan adawab kasar sun nema a daga zaben zuwa wani lokacin da zai ba da damar yin gyara gyare ga tsarin demokradiyar kasar, inda suka ce yin hakan zai tabbatar da gudanar da zabe mai inganci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.