Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane 15 sun rasu a fadan da aka yi tsakanin Boko Haram da sojoji a Kano

Jami’an tsaro a birnin Kano da ke arewacin tarayyar Najeriya, a yau lahadi sun ce sun kai hari a kan maboyar wasu da ake zargin cewa magoya bayan kungiyar Boko Haram ne a wata unguwa da ke birnin inda suka yi bata-kashi har ma aka samu asarar rayukan mutane akalla 15.

Wani hari da aka taba kai wa a Kano
Wani hari da aka taba kai wa a Kano REUTERS/Stringer
Talla

Wani kwamandan soja a rundunar wanzar da tsaro a Kanon mai suna Burgediya Janar Ilyasu Abba, ya bayyana wa manema labarai cewa 14 daga cikin wadanda suka rasa rayukansu magoya bayan kungiyar Boko Haram ne, yayin da soja daya ya rasa rayuwarsa a gumurzun.
To sai dai har yanzu babu wata kafa mai zaman kanta ta za ta tabbatar da dalilan kai harin da kuma hakikanin abin da ya faru a inda wannan lamari ya faru, yayin da Burgediya Janar Abba ya ce tuni sojoji suka yi amfani da buldoza domin rusa gidan da mutanen ke suka mayar a matsayin maboyarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.