Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan bindiga sun kashe Mutane 5 a Kano da wasu mutane 18 a Damboa

Wasu ‘yan bindigan kan babura, sun kashe mutane 5, bayan da suka bude wuta kan masu wasan Dara, a birnin Kano da ke arewacin Najeriya. kamar yadda a Jahar Borno wasu ‘Yan bindiga suka bude wuta, tare da hallaka mutane 18 a wata kasuwar garin Damboa.

Wani hari da aka kai a Kano
Wani hari da aka kai a Kano REUTERS/Stringer
Talla

Shedun gani da ido, sun ce wasu mutanen Biyu sun sami raunika, sakamakon harin da ‘Yan Bindigar suka kai a unguwar Dakata, da ke da cunkoson jama’a.

Mai Magana da yawun rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano, Magaji Majia, ya tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai bai yi Karin bayani game da mutane da suka mutu ba.

Wannan harin kuma na zuwa ne bayan Gwamnatin Jahar Kano ta haramta amfani da Baburan haya, a wani yunkurin kawo karshen tashe-tashen hankula a jihar da ke da yawan jama’a fiye da sauran jahohin arewacin kasar.

A Jahar Borno yankin Arewa maso Yammaci an samu rahoton mutuwar mutane 18 bayan da ‘Yan Bindiga suka bude wuta a wata kasuwar birnin Damboa.

Wani basaraken da ke yankin mai suna Abba Ahmad yace maharan sun bude wa wasu mafarauta ne wuta.

Akwai rahotanni masu karo da juna, kan dalilin harin, inda wasu mutanen ke cewa maharan na kyamar sayar da naman Alade da mafarautan ke yi, kamar yadda addinin musulanci ya haramta, wasu kuwa na cewa maharan na mayar da martani ne, kan yadda mafarautan suka kafa kungiyar sinturin da ke fito-na-fito da ‘Yan bindiga a yanki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.